Home Labaru Atiku Abubakar Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga Hukumomin Tsaro

Atiku Abubakar Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga Hukumomin Tsaro

76
0

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya nuna rashin jin daɗin sa bisa kisan mutanen da aka yi a jihar Zamfara.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafin san a Facebook, Atiku ya jajanta wa iyalan waɗanda kisan kiyashin ya shafa, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro su kara matsa ƙaimi wajen kawo karshen ta’addanci a Nijeriya.

Atiku Abubakar, ya mika sakon ta’aziyya da jaje ga gwamnati da kuma al’ummar jihar Zamfara bisa kisan kiyashin da akai wa mutane a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.