Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Bude Wa Masallata Wuta A Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Bude Wa Masallata Wuta A Jihar Katsina

5
0

Rahotanni daga jihar Katsina sun nuna cewa, an kashe aƙalla masallata 10, tare da kona gidaje da dama yayin da wasu ‘yan bindiga su ka afka ƙauyen Yasore da ke ƙaramar hukumar Batsari.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da mutanen su ke gudanar da sallar Magriba, inda ba zato ba tsammani ‘yan bindigar su ka buɗe masu wuta.

Tuni dai aka gudanar da jana’izar waɗanda su ka rasu da safiyar ranar Larabar da ta gabata, yayin da waɗanda su ka ji raunuka aka kai su asibiti.

Da ya ke tabbatar da harin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce maharan sun kai harin ne domin ɗaukar fansa a kan ‘yan banga.