Home Labaru Buhari Ya Bukaci N644.3M Matsayin Kudin Abinci, N76.6M Na Kudin Haya

Buhari Ya Bukaci N644.3M Matsayin Kudin Abinci, N76.6M Na Kudin Haya

25
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da jerin kudaden da ya ke bukatar kashewa a Fadar shugaban kasa a shekara ta 2022.

Kasafin kudin fadar shugaban kasa dai ya hada da Naira Biliyan 12 da Miliyan 31 na kula fadar, yayin da aka bukaci Naira Biliyan 24 da Miliyan 83 domin ayyukan sashen shugaban kasa, sannan ofishin mataimakin shugaban kasa zai kashe Naira Biliyan 1 da Miliyan 18.

Cikakken bayani a kan kudaden ya nuna cewa, an ware Naira Miliyan 644 da dubu 300 domin abinci da kayan shakatawa, sannan za a kashe Naira Miliyan 76 da dubu 600 domin biyan kudin haya.

Kudin danyen kayan abinci da alatun girki sun kama Naira Miliyan 135 da dubu 66, sannan za a kashe naira Miliyan 301 da dubu 13 na danyen kayan abinci da alatun girki na gidan shugaban kasa, yayin da aka ware naira Miliyan 156 da dubu na danyen kayan abinci da alatun girki na gidan mataimakin shugaban kasa.