Home Labaru Babu Dan Takarar Kudu Da Zai Iya Lashe Zabe – Dokpesi

Babu Dan Takarar Kudu Da Zai Iya Lashe Zabe – Dokpesi

22
0

Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP Cif Raymond Dokpesi, ya ce babu wani dan takara daga yankin kudu da zai iya lashe wa jam’iyyar zaben shugaban kasa na shekara ta 2023.

Raymond Dokpesi ya bayyana haka ne, a cikin wata hira da jaridar Daily Trust ta buga, inda ya ce babu wani dan takara daga kudu maso gabas da zai iya cin nasara a zaben shekara ta 2023 a kan dan arewa.

Sai dai ya ce duk wanda ya zama shugaban kasa dole ne ya yi dannar kirji ga mutanen kudu maso gabas, amma ya ce ya kamata jam’iyyar PDP ta nemi dan takarar ta daga yankin arewa.