Home Labaru Yaki Da Talauci: Shugaban Kasa Buhari Ya Yiwa ‘Yan Najeriya Albishir

Yaki Da Talauci: Shugaban Kasa Buhari Ya Yiwa ‘Yan Najeriya Albishir

171
0
Shugaba Muhammadu-Buhari-2
Shugaba Muhammadu-Buhari-2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen talauci a Najeriya da kuma karfafa fannin noma.

Shugaban kasa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da kudurin da yake dashi a zangon mulkinsa na biyu nashi karo, inda ya bukaci matasan Najeriya  su kara kaimi a fannin noma domin shi ne jigon arziki a kowacce kasa ta duniya.

Shugaban kasa  Buhari,  ya ce wannan zangon zai yi amfani dashi wajen cika alkawuran da ya dauka lokacin zabe akan tattalin arziki da tsaro.

Ya ce ya kamata kowa ya san abinda na sanya a gaba, saboda gwamnati za ta fara aiki akan alkawuran da ta dauka a bangaren matsalar tsaro da tattalin arziki, da cin hanci da rashawa.

Sannan kuma ya yi alkawarin sa mutumin kirki a matsayin ministan ayyukan  gona domin amfani da bangaren wajen samarwa ‘yan Najeriya aiki.

Shugaban kasa  ya sha alwashin inganta rayuwar manoman Najeriya domin samun abinci mai yawa , inda ya mika godiyar akan yadda matasan Najeriya suka dage da noma.