Home Labaru Dakile Hari: Hazikan Sojoji 3 Sun Kwanta Dama

Dakile Hari: Hazikan Sojoji 3 Sun Kwanta Dama

283
0

Rahotanni sun ce  wasu jami’an soji uku sun mutu a lokacin da dakarun Operation lafiya dole suka dakile harin ‘yan ta’addan Boko Haram a kauyen Molai da ke jihar Borno.

Dakarun sun fafata da ‘yan ta’addan ne a wani musayar wuta da suka yi a Mammanti, wani kauye kusa da Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

‘Yan ta’addan da suka fito da dama na kan hanyar su ce na kai farmaki Molai, kilomita biyu daga babbar birnin jihar kafin suka fara musayar wuta. An ce karan tashe-tashen bama-bamai da alburusai a tsakar dare ya jefa mazauna Molai da wasu yankunan Maiduguri cikin wani hali.