Home Labaru Tsaro: Rundunar Soji Ta Sauya Kwamandan Rundunar Lafiya Dole

Tsaro: Rundunar Soji Ta Sauya Kwamandan Rundunar Lafiya Dole

321
0

Rundunar sojin Najeriya ta nada sabon kwamanda da zai jagoranci wata babbar rundunar atisaye da ke Maiduguri a jihar Borno.

Rundunar ta nada Birgediya Janar AK Ibrahim, kwamanda a runduna ta 7 dake Maiduguri a matsayin sabon kwamandan runduna ta 1 a karkashin atisayen ‘Ofireshon Lafiya Dole’.

A cikin wata daga ofishin sakataren rundunar soji, Birgediya Janar Ibrahim zai karbi aiki ne daga hannun Manjo Janar Bulama Biu, wanda ke jagorantar runduna ta 3 ta sojojin hadin gwuiwar kasashen gefen tefkin Chadi.

Kazalika an sanar da yi wa Manjo Janar CG Musa da B.A Akinroluyo sauyin wurin aiki zuwa sashen rundunar sojoji dake Minna a jihar Neja.