Rundunar sojin Nijeriya, ta kafa wani babban sansani a Kotonkoro da ke karamar hukumar Mariga a jihar Neja, domin magance matsalar garkuwa da mutane da fashin shanu da kuma ayyukan ‘yan bindiga a yankin.
Kwamandan runduna ta 31 da ke Minna Birgediya Janar Gideon Ajetonmobi ya bayyana haka, yayinda yake kewayawa da babban sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Matane yayin wata ziyarar ban-girma.
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na sakataren gwamnatin jihar Lawal Tanko ya fitar,Janar Ajetonmobi yace an kafa sansanin ne domin magance rashin tsaro da ya addabi yankin da wasu yankunan jihar.
Ya ce akwai bukatar kafa sansanin sojin, tunda jihar ta yi iyaka da jihohin Zamara da Kebbi, ya na mai cewa, sansanin zai kawo mafitar da ake bukata akan hada-hadar‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da barayin shanu daga jihohin da ke makwaftaka da jihar Neja.