Home Labaru Ta’addanci: An Sace Shugaban Jam’iyyar AA A Birnin Abuja

Ta’addanci: An Sace Shugaban Jam’iyyar AA A Birnin Abuja

162
0

Wasu gungun mutane da ba a san ko suwanene ba, sun yi garkuwa da shugaban jam’iyyar AA a harabar bankin Zenith da ke Dutse a birnin tarayya Abuja.

Mai dakinsa ta bayyana wa manema labarai cewa, maigidanta ya tashi da sassafe, inda ya ga an yi ta kwashe masa kudi a asusun ajiyar sa na bankin Zenith, inda a cikin gaugawa ya garzaya domin kai wa hukumar Bankin kuka a kan abin ke faruwa.

Ta ce isarsa ke da wuya, sai kawai wasu a cikin babbar mota kirar SUV suka kama shi tun daga waje suka saka shi cikin motar suka tafi da shi.

Idan daiba a manta ba, jam’iyyar AA ita ce jam’iyyar da tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha ya tsaida surukinsa takarar gwamnan jihar Imo.