Home Labaru Wata Sabuwa: Dokar Nijeriya Ba Ta Yarda A Wallafa Sakamakon Zabe A...

Wata Sabuwa: Dokar Nijeriya Ba Ta Yarda A Wallafa Sakamakon Zabe A Yanar Gizo Ba – INEC

260
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta Kasa, INEC

Daraktan yada labarai na hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC Oluwole Osaze-Uzzi, ya ce dokar Nijeriya ba tayi wani tanadi na sanya sakamakon zabe a shafin yanar gizo ba.

Daraktan yada labarai Oluwole Osaze-Uzzi

Osaze-Uzzi ya bayyana haka ne, yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels a cikin shirin siyasarmu a yau da ake gabatarwa duk ranar Alhamis.

Ya ceko da a ce Nijeriya ta fara amfani da hanyar zabe ta zamani tare da fitar da sakamako, wadanda ke son kawo tangarda ga lamarin ba fasawa za suyi ba.

Osaze ya kara da cewa, kowa zai iya sanya sakamakon zabe a shafin yanar gizo, kuma idan har ‘yan Nijeriya na so a yi hakan za a iya yi, amma babu tabbacin cewa ba za a iya samun  tangarda ga sakamakon ba.