Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kara zage damtse wajen yakar ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram baki daya musamman a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Sabon kwamandan rundunar ta musamman dake yaki da ta’addancin kungiyar da ake yiwa lakabi da Operation Lafiya Dole ya tabbatar da haka a wajen birne gawarwakin wasu jami’an soji 5 da suka rasa rayukansu a jihar Borno.
Ya ce akwai shirye-shirye da aka samar wajen tabbatar da cewa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu basu sha wahala wajen kula da jin dadinsu ba.














































