Home Labaru Tsaro: Rundunar Soji Ta Bukaci Mutanen Yankin Kudu Maso Gabas Kada Su...

Tsaro: Rundunar Soji Ta Bukaci Mutanen Yankin Kudu Maso Gabas Kada Su Razana Da Yawaitar Jami’anta

183
0
BORNO, NIGERIA - MARCH 29: Nigerian soldiers are seen after an operation against Boko Haram terrorists at a terrorist camp in Borno, Nigeria on March 29, 2016. (Photo by Stringer/Anadolu Agency/Getty Images)

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta bukaci al’ummomin yankin kudu maso gabashin Najeriya kada su razana da yawaitar zirga-zirgar jami’anta, ababen hawa da kuma makamanta a yankin na tsawon mako guda.

Kanar Aliyu Yusuf

Mataimakin jami’in yada labarai da hulda da jama’a na runduna ta 82 Kanar Aliyu Yusuf , ya furta hakan a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar yau a Enugu.

Yusuf, ya ce akwai wani atisaye na tsawon mako guda da jami’an sojin za su gudanar a yankin a kokarin da suke na magance matsalar tsaro a fadin Najeriya.

Ya ce dukkanin atisayen za a gudanar dasu ne a yankin Enugu, sai kuma atisayen harbe-harbe da za a gudanar a sansanin soji dake Owerri a jihar Imo.