Home Labaru An Jinjinawa Matashin Da Ya Mayar Da $50,000 Bayan Tsintarsu A Cikin Babur

An Jinjinawa Matashin Da Ya Mayar Da $50,000 Bayan Tsintarsu A Cikin Babur

21
0

An jinjinawa wani matashi ɗan kasar Liberia bayan ya dawo da dala dubu hamsin da ya tsinta a cikin wani babur kusa da iyakar kasar da Code d’Voire.

Matashin mai suna Emmanuel Tolue ya tarar da kudin ne da aka a saka a cikin wani kunshi kuma ya mayar wa mutumin da ya mallakin kunshi.

Mutumin ya gamu da matshin ne bayan jin kiran da ya yi ta kafar rediyo ga duk wani da ya gamu da tsabar kudi.

An ba matashin ladar dala dubu daya da dari biyar.