Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Jami’an Hana Fasa-Kwauri Sun Kama Makamai A Jihar Oyo

Yaki Da Ta’addanci: Jami’an Hana Fasa-Kwauri Sun Kama Makamai A Jihar Oyo

15
0

Jami’an hukumar kwastam sun kama albarusai 751 a cikin wata mota dake boye a garin alabo.
An kama motar ce a yayin wani sintiri da jami’an hukumar suka gudanar a yankin Igbo-Ora na Jihar Oyo.
Kwanturolan Hukumar Kwastam da ke kula da yankin, Hussein Kehinde Ejibunu, ya ce, “A cikin kayan da aka kama akwai harsasai 751 da kuma bahunan rogo da shinkafa ’yar gwamnati.
Sai dai ya ce diraban motar da yaronsa sun tsere suka bar moatar a lokacin da suka yi ido hudu da jami’an kwastam din.
Yace “Motocin da kayan suna hedikwatar hukumar domin a kara bincike”.
Ejibunu ya kuma yi kira ga jama’a da su rika taimaka wa hukumar da bayanai domin yakar ayyukan masu fasakwauri.