Home Labaru Dakile Kai Hari: Sojoji Sun Fatattaki Mayakan ISWAP A Jihar Sakkwato

Dakile Kai Hari: Sojoji Sun Fatattaki Mayakan ISWAP A Jihar Sakkwato

15
0

Sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan kungiyar ISWAP da suka kaddamar da wani hari a yankin Sabon Birni na Jihar Sakkwato.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ba wa sojojn bisa namijin kokarin, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen samar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
Hedikwatar Tsaro ta tabbatar da harin ta’addancin a kan wani sansanin soji da ke karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato inda aka kashe jami’an soji da na soji.
Daraktan yada labarai na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Benjamin Sawyer, ya ce sojojin Najeriya da na Nijar suna gudanar da aikin hadin gwiwa domin zakulo sauran mayakan na ISWAP.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa sojojin Operation Hadarin Daji tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun yi nasarar dakile harin.