Home Labaru Dakile Shigo Da Makamai: Rundunar Sojin Ruwa Bukaci Gwamnati Ta Gina Ganuwa...

Dakile Shigo Da Makamai: Rundunar Sojin Ruwa Bukaci Gwamnati Ta Gina Ganuwa Kan Iyakokin Najeriya

13
0

Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gina manyan ganuwa akan iyakokin Najeriya domin magance matsalar kwararowar makamai.

Babbar jami’ar Rundunar Jemima Malafa, wacce ta wakilci rundunar ce ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa kan wasu kudurori a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai ta kasa a nan Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daga cikin kudurori guda hudu da ake kokarin amincewa da su domin zama doka har da na neman kafa Hukumar Kula da Yaduwar Kanana da Matsakaitan Makamai ta Kasa.
Sauran sun hada da dokar takaita amfani da abubuwan fashewa, da ta neman amincewa a yi amfani da kyamarar sirri ta CCTV wajen tsaron kasa.
Kudurin karshe kuma na neman a kebe watan Nuwamba a matsayin wata na musamman domin jinjinawa jami’an tsaro a Najeriya.