Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: An Kama Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Anambra

Yaki Da Ta’addanci: An Kama Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Anambra

1062
0

Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Anambra, ta sanar da kama wasu gugun mutane hudu da su ka addabi jama’a su na yin garkuwa da su.

Mutanen da aka kama kuwa, su kan rika sa kayan sojoji domin yaudarar jama’a su na yin garkuwa da su.

Daga cikin mutane kuma akwai soja daya mai mukamin Las-Kofur, wanda ke sanye da kayan sa na sojoji a lokacin da aka kama su.

An da samu nasarar kama mutanen ne, bayan sun yi garkuwa da wani mai suna Uchenna Ezeonu a garin Ekwulobia a Jihar Anambra.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda na jihar Anambra Haruna Mohammed, ya ce an ceto wanda aka yi garkuwar da shi tun kafin a ce an yi masa wani lahani.

Wadanda aka kama kuwa sun hada da wani Obasi Peter, da Benjamin Nicholas da Ojiegbe Obinna.

Leave a Reply