Home Labaru Tsuntsu Daga Sama: Giadom Ya Zama Sakataren Jam’iyyar APC Na Kasa

Tsuntsu Daga Sama: Giadom Ya Zama Sakataren Jam’iyyar APC Na Kasa

448
0

Kwamitin gudanarwa na uwar jam’iyyar APC, ya amince da nadin Victor Giadom a matsayin sabon mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa.

An dai nada Giadom ne domin ya maye gurbin tsohon sakataren jam’iyyar Mai Mala Buni, wanda yanzu haka shi ne zababben gwamnan jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar APC Lanre Issa-Onilu ya fitar, ta ce Giadom zai kasance sakataren rikon-kwarya har zuwa lokacin da jihar Yobe za ta fidda da wanda zai gaji Buni a matsayin sakatare mai cikakken iko.

Kafin a nada shi a matsayin sakataren rikon-kwarya, Giadom, wanda dan asalin jihar Ribas ne, shi ne mataimakin sakataren jam’iyyar APC na kasa.

Ya kuma taba rike mukamin shugaban karamar hukumar Gokana ta jihar Rivers, kafin daga bisani tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya nada shi a matsayin kwamishina daga shekara ta 2011 zuwa 2015

Leave a Reply