Home Labaru Tashin Farko: Matawalle Ya Lashi Takobin Magance Matsalar Tsaro A Jihar Zamfara

Tashin Farko: Matawalle Ya Lashi Takobin Magance Matsalar Tsaro A Jihar Zamfara

641
0

Gwamnan jihar Zamfara mai jiran gado Dakta Muhammad Bello Matawalle Maradun, ya ce rashin adalci ya na daga cikin manyan dalilan da su ka haifar da rashin tsaro a jihar Zamfara.

Sabon gwamnan, wanda tsohon shugaban kwamitin tsaro ne a majalisar wakilai, ya ce kwarewar sa ta sa ya fahimci hanyoyin da zai bi wajen kawo karshen matsalar tsaro da jihar Zamfara ke fama da ita.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Asabar da ta gabata ne, hukumar zabe ta kasa ta bayyana Matawalle na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce wannan ya na zuwa ne bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, inda ta soke guraben duk ‘yan takarar jam’iyyar APC na jihar Zamfara.

Leave a Reply