Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya ce har yanzu hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ba ta da tsayayyen shugaba, saboda gwamnatin Buhari ta gaza maye gurbin Ibrahim Magu a lokacin da majalisar ta ki amincewa da sunan sa.
Saraki ya bayyana haka ne, yayin wani bikin wayar da kan zababbun ‘yan majalisar tarayya da za su shiga majalisa ta 9.
Ya ce ya zama wajibi gwamnatin shugaba Buhari ta bi matakan da su ka dace na ko dai ta sake gabatar da sunan wani ko kuma ta bi hanyar zagaye shugabannin majalisar dattawa a siyasance.
Saraki ya shaida wa zababbun ‘yan majalisar su sani cewa ,majalisar dattawa na da karfin ikon tabbatarwa, ko kuma kin tabbatar da sunayen da shugaban kasa zai gabatar masu a kan nadin wani mukami. Saraki ya yi nuni da cewa, mummunan kallon da jama’a ke yi wa majalisar tarayya ya sa har majalisar ta 8 ta yi bakin jini, duk da cewa ta na gudanar da ayyukan ta ne bisa tsarin doka.
You must log in to post a comment.