Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Da Dama A Jihar Zamfara

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Da Dama A Jihar Zamfara

534
0

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu satar shanu da garkuwa da jama’a ne, sun kashe akalla manoma 10 a jihar Zamfara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta tabbatar.

‘Yan bindigar dai, sun kai farmaki ne a wata gonar albasa da ke kauyen Kwari na karamar hukumar Shinkafi, inda su ka harbe manoman da ke bakin aiki kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar Mohammed Shehu ya bayyana.

Mohammed. ya ce sun baza jami’an tsaro domin maido da zaman lafiya a yankin, amma bai yi karin bayani a kan musabbabin harin ba, sai dai ana ganin hakan bai rasa nasaba da harin ramako, lura da cewa a ‘yan kwanakin nan ne sojoji su ka fatattaki barayin shanun daga maboyar su.

Makwanni biyu kenan da sojojin su ka kai samame a sansanonin ‘yan bindigar, inda su ka hallaka kwamandojin su kamar yadda wani mazaunin kauyen Kwari Hashimu Abu ya bayyana.

Leave a Reply