Home Labaru Hatsarin Jirgi: Da Na Mutu Da Mutane Da Dama Sun Shiga Tsomomuwa...

Hatsarin Jirgi: Da Na Mutu Da Mutane Da Dama Sun Shiga Tsomomuwa – Osinbajo

326
0
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce in da ya hadu da ajalin sa yayin da ya yi hatsarin jirgi sama, da wadanda aka dora wa nauyin kula da tsaron sa sun shiga cikin tsomomuwa.

Idan dai za a iya tunawa, Farfesa Osinbajo ya yi hadarin jirgin sama ne a Kabba ta Jihar Kogi ranar 2 Ga Fabrairu, sai dai shi da sauran mutanen da ke cikin jirgin babu wanda ya samu rauni sosai.

Osinbajo ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke jawabi a wajen taron taya Shugaba Muhammadu Buhari da shi kan sa murnar sake lashe zabe a Cocin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Ya ce in da rayuwar su ta salwanta a hatsarin, da ita kan ta gwamnatin Jihar Kogi ta shiga tsomomuwa.