Kungiyar daliban kasar nan ta yi barazanar fallasa wasu al’amuran rashawa a NDDC.
Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da cewa ya karbi bayanan kashe kudin hukumar don gudun zagon kasa ga kokarinsa.
A wata takarda da aka mika ga manema labarai shugaban kungiyar Kwamared Danielson Bamidele Akpan ya tabbatar da cewa daliban Najeriya za su yi zanga-zanga matukar wani ya yi kokarin zagon kasa ga kokarin da gwamnati ke yi na yaki da rashawa.