Home Labaru Kiwon Lafiya Jaje: Gwamnatin Tarayya Ta Aikawa Sarkin Saudiyya Wasika

Jaje: Gwamnatin Tarayya Ta Aikawa Sarkin Saudiyya Wasika

215
0

Shugaba Muhammadu Buhari na ya aikawa Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz da wasika bayan da aka kwantar da basaraken a asibiti.

SHUGABA BUHARI DA SARKIN SAUDIYYA

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannun mai Magana da fadarsa Malam Garba Shehu.

Shugaban yace gwamnati da kuma mutanen Najeriya nayi wa sarkin Saudiyya fatan warkewa cikin gaggawa.

Buhari ya jaddada cewa “Sarki Salman babban aboki ne ga Najeriya kuma bai taba kin taimaka wa kasar nan ba a lokacin bukata, saboda haka ina fatan ya samu sauki cikin gaggawa.

kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya bayanna cewa an kwantar da sarkin a wani asibiti da ke Birnin Riyadh sanadiyyar fama da yake yi da matsalar mafitsara.

Tun shekarar 2015 sarkin mai shekaru 84 ya ke mulkin kasar ta Saudiyya.