Home Labaru Yaki Da Manyan Laifuka: ‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri A...

Yaki Da Manyan Laifuka: ‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri A Jihar Legas

248
0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama aƙalla mutum 15 bisa zargin su da zama ƙungiyoyin asiri da kuma ta’addanci a jihar.

Har ila yau, rundunar ta ƙwato miyagun makamai daga hannun gungun mutanen da ke addabar mazauna yankunan Lekki da Ajah.

Kakakin rundunar Muyiwa Adejobi

Kakakin rundunar Muyiwa Adejobi ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a dai dai lokacin da kokarin aikata laifukan.

Ya ce jami’ansu sun kama wani matashi mai shekara 20 mai suna Taiye Lasisi ranar Litinin ɗauke da bindiga ƙirar gida bayan an nemi agajinsu a yankin Ikorodu.

Bayan kama shi ne kuma aka tsananta bincike, inda aka kama wasu mutum 13 ‘yan ƙungiyar asiri ta Aiye Confraternity, a cewar Mista Adejobi.

Ya ƙara da cewa sun sake kama wani ɗan ƙungiyar asirin mai suna Lekan Razak mai shekara 20 yayin da yake yunƙurin aikata fashi a kan Titin Ibomide da ke Lekki.