Home Labaru Shekarar 2020: Kungiyar RSF Ta Yi Allah Waddai Da Kisan ‘Yan Jaridu...

Shekarar 2020: Kungiyar RSF Ta Yi Allah Waddai Da Kisan ‘Yan Jaridu 50

318
0

Kungiyar ‘yan jaridun kasa da kasa ta Reporters Without Borders ta koka da yadda ‘yan jaridu 50 suka rasa rayukansu cikin shekarar da muke bankwana da ita ta 2020, galibinsu a kasashen da basa fuskantar rikici ko yaki.

Alkaluman da kungiyar ta fitar ya nuna yadda aka samu karuwar kashe ‘yan jarida a bakin aiki, musamman masu binciken kwakkwaf kan abubuwan da suka shafi manyan laifuka da cin hanci da rashawa da kuma gurbacewar muhalli.

Rahoton kungiyar ta Reporters without Borders ya ce kasashen Mexico da India da kuma Pakistan su ne kan gaba wajen kisan ‘yan jaridun a bana.

Rahoton wanda RSF ke fitarwa a karshen kowacce shekara, ta ce an samu karuwar kisan ‘yan jaridun da kashi 85 idan aka kwatanta da kashi 63 da aka samu a shekarar 2019.

Haka zalika RSF ta ce cikin 2020 akalla ‘yan jarida 387 aka daure a gidajen yari ciki har da ‘yar jaridar China Zhang Zhan da kotu da aike yari na tsawon shekaru 5 baya ga wasu a Saudi Arabia.