Home Labaru Hukunci: Kotu Ta Ba Da Umarnin Yi Wa Matasa A Kano

Hukunci: Kotu Ta Ba Da Umarnin Yi Wa Matasa A Kano

342
0

Wata Kotun Majistire da ke Kano ta yanke wa wasu maza biyu, hukuncin bulala 12 ga kowannensu sakamakon samunsu da tabar wiri da wasu kayan maye.

Matansa biyu Muhammad Sani mai shekaru 24 da Saddam Ali mai shekaru 24 sun gurfana a gaban kotun ne bisa laifin mallakar tabar wiwi da wasu ababe masu gusar da hankali.

Alkalin Kotun, Farouk Ibrahim, ya yankewa matasan hukuncin ne bayan sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.

Alkali Ibrahim ya umarci da a yi wa kowanen su bulala 12 bayan sun roki kotun da ta yi musu sassauci.

Jami’in dan sanda wanda ya gabatar da kara, Mista Muhammad Bichi, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne da misalin karfe 9.00 na safiya a ranar 21 ga watan Dasimba a Unguwar Plaza da ke Karamar Hukumar Fagge a Kano. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nigeria NAN ya ruwaito, jami’in dan sandan na cewa laifin da matasan suka aikata ya saba wa sashe na 403 cikin dokokin Jihar Kano