Home Coronavirus Yaki Da COVID-19: Buhari Ya Tafi Nijar Halartar Taron ECOWAS

Yaki Da COVID-19: Buhari Ya Tafi Nijar Halartar Taron ECOWAS

311
0

A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi Jamhuriyar Nijar domin halartar taron shugabannin kungiyar raya tattalin Arzikin yammacin afirka (ECOWAS) kan yaki da cutar Coronavirus.

A watan Afrilu kungiyar ECOWAS ta nada shugaban kasa Buhari a matsayin shugaban kwamitinta na yaki da cutar, wanda zai gabatar da rahoto a taron na yini guda.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ce shugabn kasa Buhari zai jagoranci yakar annobar cutar coronavirus a Yammacin Afirka.

Zauren shugabannin ECOWAS ya kuma zabi ministocin Najeriya na lafiya da sufurin jiragen sama da na kudi a matsayin shugabannin kwamitocin da suka shafi ma’aikatunsu, wanda shugaban kasa Buhari zai jagoranta domin samun nasara a yaki da coronavirus.

Taron zai kuma karbi rahoto akan samar da takardar kudin bai-daya na ECOWAS daga Julius Midara na kasar Saliyo da kwamitin sa.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Jean Claude Kassi Bou, zai gabatar wa taron rahoton wucin gadi a kan Muradun ECOWAS na shekarar 2050 da sauransu.

Sauran batutuwan da taron zai tattauna sun hada da karuwar matsalar tsaro a yankin da kuma rikicin siyasar kasar Mali.

Leave a Reply