Home Labaru Tallafi: Gwamnatin Tarayya Ba Za Ta Iya Ci Gaba Da Kashe Naira...

Tallafi: Gwamnatin Tarayya Ba Za Ta Iya Ci Gaba Da Kashe Naira 5 A Kowanne Wata Ga ‘Yan Gudun Hijira – Majalisa

156
0
Takaddama: Dokar Kariya Ta Raba Kawunan ‘Yan Majasalisar Tarayya
Takaddama: Dokar Kariya Ta Raba Kawunan ‘Yan Majasalisar Tarayya

Kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattawan Najeriya, ta ce gwamnatin tarayya na kashe naira biliyan biyar a kowanne wata a kan ‘yan gudun hijira da ke yankin arewa maso gabas.

An kafa sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin saboda tsanantar al’amuran mayakan ta’addancin Boko Haram.

A na ci gaba da rasa rayuka tare da kadarori sakamakon yadda mayakan ta’addancin suka addabi yankin.

A yayin zantawa da manema labarai shugaban kwamitin Yusuf Yusuf,, ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da kashe wannan makuden kudaden ba akan ‘yan gudun hijira.

Sanatan ya ce dole ne kowanne mataki na gwamnati ya tabbatar da dawowar ‘yan gudun hijira zuwa yankunansu, saboda akwai mutane fiyea da milliyan 2 a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke jihohin arewa maso gabas.

Abinda ya kamata shi ne aiki tare, ta  yadda tsaro ya na da matukar amfani.

Leave a Reply