Home Labaru Yadda ‘Yan Damfara Su Ka Nemi Handame Shinkafar ‘Yan Gudun Hijira

Yadda ‘Yan Damfara Su Ka Nemi Handame Shinkafar ‘Yan Gudun Hijira

277
0

Hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya, ta nuna takaicin yadda wasu ‘yan damfara su ka yi kokarin handame shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta ware domin raba wa ‘yan gudun hijira da masu karamin karfin da ba su iya ciyar da kawunan su.

Kakakin Yada Labaran hukumar na Shiyyar Minna ta Jihar Neja Joseph Attah ya bayyana wa manema labarai haka.

Attah ya ce, gwamnati ta kafa kwamitin raba shinkafar da kwastan su ka kama ta ga sansanonin gudun hijira da gidajen marayu, tare da bada labarin yadda mutane su ka rika kai takardun bogi masu nuna su na da gidajen marayun da su ke ciyarwa.

Ya ce sun ce kowa ya kai takardun shaidar ya na da gidajen marayun da ya ke ciyarwa, inda a cikin kankanen lokaci su ka karbi takardu har 56, amma daga cikin 30 da su ka tantance 6 ne kawai sahihai, sauran 34 duk ‘yan wala-wala ne.

Joseph Attah ya kara da cewa, akwai wani mutum da ya ce ya na ciyar da gajiyayyu, amma da aka bi shi don gani da ido sai ya kai su wani masallaci, wai a can ya ke ciyar da mutane.

Leave a Reply