Mutane da dama ake fargabar sun rasa rayukan su, a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun a yankin Wukari na Jihar Taraba.
Rahotanni sun ce yanzu haka rikicin ya haddasa gagarumar asara a kauyukan kabilun biyu, ciki har da Wukari-Kwatan-Sule da Chonku da kuma iyakokin garuruwan Jootar da Vaase.
Shugaban kabilar Jukun Bako Benjamin ya shaida wa manema labarai cewa, duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da su ka cimmawa da kabilar Tibi a makon da ya gabata, har yanzu su na ci-gaba da kai masu farmaki.
A cewar sa, da sanyin safiyar Asabar da ta gabata ne, ‘yan kabilar Tibi su ka sake kai farmaki a kauyukan su tare da kone gidaje, baya ga kisan wasu mutane 15, matakin da ya sa matasan kabilar Jukun su ka maida martani.
Tuni dai Rundunar ‘yan sanda ta jihar Taraba ta tabbatar da afkuwar rikicin, inda ta ce jami’an ta su na kokarin kwantar da hankulan mutane.
You must log in to post a comment.