Home Labaru Dele Momodu Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar

Dele Momodu Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar

12
0

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NCP Bashorun Dele Momodu ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Momodu ya bayyana sauya shekar ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da ya ke neman yafiyar ‘yan Nijeriya bisa rawar da ya taka wajen kawo gwamnatin jam’iyyar APC.

Ya ce ya ɗauki matakin shiga PDP ne don ya bada gudummuwa a haɗa karfi da karfe wajen ceto Nijeriya daga rugujewa.

Dele Momodu, ya ce abin takaici da kuma da-na-sani shi ne, wasu manyan nasarorin da jam’iyyar PDP ta yi a zamanin mulkin ta yanzun gwamnatin APC ta lalata komai.

Tsohon dan jaridar, ya ce ya na neman afuwa game da rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarar shugaba Muhammadu Buhari a shekara ta 2015.