Home Labaru Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Rutsa ‘Yan Fashi A Wani Banki Da...

Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Rutsa ‘Yan Fashi A Wani Banki Da Ke Abuja

349
0
Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Rutsa ‘Yan Fashi A Wani Banki Da Ke Abuja

Rundunar ‘yan sanda ta dakile yunkurin wasu ‘yan fashi da su ka afka wa Bankin First Bank a Abuja ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni na cewa, aikin hadin gwiwa ne tsakanin ‘yan sanda da ‘sojoji, inda su ka harbe daya daga ‘yan fashin, sannan su ka kama wasu hudu a harabar ginin Bankin da ke Mpape a Abuja.

Jami’an tsaron sun zagaye ginin Bankin ne, sannan su ka rutsa ‘yan fashin a ciki na tsawon sa’o’i da dama. Wasu hotuna da bidiyo da su ka karade shafukan sada zumunta na zamani, sun nuna yadda ‘yan sandan su ka kama wasu daga cikin ‘yan fashin.