Home Labaru Cin Bashi: Baitulmalin Nijeriya Ya Na Barazanar Karewa – Obasanjo

Cin Bashi: Baitulmalin Nijeriya Ya Na Barazanar Karewa – Obasanjo

256
0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa Nijeriya ta na fuskantar barazanar karewar baitulmali, sakamakon karuwar adadin bashin da gwamnati ke karba.

Obasanjo, ya yi gargadin ne a wajen wani taron addini da ya gudana a Legas, inda ya koka da yadda Nijeriya da wasu kasashen Afrika ke ciwo bashi daga bankin duniya da asasun IMF da sauran hukumomi, matakin da ya ce idan ba a yi taka-tsantsan ba zai tagayyara tattalin arzikin su.

Tsohon shugaban kasar, ya kuma ja hankali kan kididdigar da ta nuna cewa, zuwa karshen watan Maris na shekara ta 2019, adadin bashin da ake bin Nijeriya ya kai dala biliyan 81 da miliyan 274.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta sha kare kan ta da cewa, ta na karbo bashin ne domin cike gibin bukatun gudanar da ayyukan raya kasa.