Home Labaru Albashi: Gwamnoni Sun Bukaci A Sauya Yadda Ake Rabon Dukiyar Kasa

Albashi: Gwamnoni Sun Bukaci A Sauya Yadda Ake Rabon Dukiyar Kasa

331
0
Albashi: Gwamnoni Sun Bukaci A Sauya Yadda Ake Rabon Dukiyar Kasa
Albashi: Gwamnoni Sun Bukaci A Sauya Yadda Ake Rabon Dukiyar Kasa

Gwamnonin Nijeriya, sun nemi a sauya yadda ake rabon kudaden kasa idan har za su biya ma’aikatan su mafi karancin albashi na Naira dubu 30.

Duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar biyan mafi karancin albashin hannu, amma har yanzu akwai jihohin da ba za su iya biya ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya ce wasu jihohin ba su da karfin da wasu ke da shi, don haka akwai yarjejeniyar da gwamnatin tarrayya ta yi da Kungiyar Kwadago, wanda ba lallai ne jihohi su amince da hakan ba. Ya ce su na kan bakan su na neman a sauya yadda ake rabon dukiyar kasa, wanda aka fara tun shekaru kusan 20 da su ka wuce, kuma tun lokacin ne gwamnonin ke kokawa akan haka, duk da ya zama dole su bi dokar da ta ce a biya ma’aikata, amma za su cigaba da neman a yi gyaran da zai taimaka wa kasa.