Home Labaru Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda – IG Adamu

Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda – IG Adamu

484
0
Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda-IG Adamu
Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda-IG Adamu

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya ce shafukan sada zumunta sun sama babbar matsala da ke cima rundunar ‘yan sanda tuwo a kwarya.

Muhammad Adamu ya kara da cewa, matsala shafukan sada zumunta ta dade ta na cima ‘yan sanda tuwo a kwarya musamman a wannan lokaci.

Adamu ya bayyana haka ne a lokacin taron wayar da kai, da aka shiryawa jami’an hulda da jama’a na hukumar da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, wanda ya gudana a jihar Anambra.

Shugaban ‘yan sanda ya ce, hanyoyin sadarwa sun sauya zuwa na zamani, wanda su keiya gyarawa abubuwa ko lalata zaman-takewa.

A karshe Muhammad Adamu ya gargadi mahatarta taron da cewa, a matsayin ku na jami’an ‘yan sanda aikin ku shi ne kare mutuncin aikin dan sanda a ko da yaushe, sannan za ku iya amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen gudanar da ayyukan ku yadda ya kamata.