Home Labaru Sarki Sanusi Ya Yabawa Ganduje A Kan Shirin Bayar Da Ilimi Kyauta...

Sarki Sanusi Ya Yabawa Ganduje A Kan Shirin Bayar Da Ilimi Kyauta A Kano

513
0
Sarki Sanusi Ya Yabawa Ganduje A Kan Shirin Bayar Da Ilimi Kyauta A Kano
Sarki Sanusi Ya Yabawa Ganduje A Kan Shirin Bayar Da Ilimi Kyauta A Kano

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abdullahi umar Ganduje sakamakon bullo da shirin bada ilimin frimare da sakandare kyauta a fadin jihar.

Wata majiya ta ce, duk da sa-in-sa da ke tsakanin su, an ji sarki Sanusi na cewa, wannan shine irin abinda Nijeriya ke bukata domin cigaban ilimi.

Sarki Sunusi na II ya kara da cewa abinda gwamnan Ganduje ya yi abin koyi ne, kuma an yi ne domin cigaban al’umman, sannan muna fatan wasu jihohin su za yi koyi da irin wannan sallon mulki na mai girma gwamna Ganduje.

Sanarwar ta kuma ce, ya kamata gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki su hada kai wajen ganin al’ummar su sun zama abun alfahari.

Sarkin Sunusi ya yi wannan yabon ne lokacin da gwamnan ya ke ganawa da wata tawaga daga bankin Zenith karkashin jagorancin shugaban yankin Arewa maso yamma Sani Yahaya.