Home Labaru NNPC Ta Ce Ta Gano Man Fetur Da Iskar Gas Yankin Arewa...

NNPC Ta Ce Ta Gano Man Fetur Da Iskar Gas Yankin Arewa Maso Gabas

388
0
NNPC Ta Ce Ta Gano Man Fetur Da Isakar Gas Yankin Arewa Maso Gabas
NNPC Ta Ce Ta Gano Man Fetur Da Isakar Gas Yankin Arewa Maso Gabas

Hukumar kula da albarkatun mai ta kasa NNPC ta ce ta gano mai a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Mukadashin manajan sashin hulda da al’umma na kamfanin, Samson Makoji ya sanar da haka a ranar juma’ar da ta gabata.

Makoji ya kara da cewa, an gano man fetur da iskar gas masu tarin yawa a yankin Gongola, wanda hakan zai taimaka wajen janyo masu sa hannun jari zuwa Nijeriya, tare da samar da guraban ayyuka da kuma inganta hanyoyin samun kudin shiga ga gwamnati.

Hukumar ta kuma ce, ta gano bakunan mai masu yawa a rafin kolmani II da Upper Benue da Gongola a yankin arewa maso gabas.

Idan dai ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara hakar mai a rafin Kolmani II a ranar 2 ga watan Fabrairun shekara ta 2019.

Makoji ya cigaban da cewa, an hako daya daga cikin rijiyoyin tare da gano man fetur da iskar gas a matakai daban-daban.