Home Labaru Yada Labarai: Gwamnati Za Ta Ba Tashoshin Rediyo Da Talabijin Na Yanar...

Yada Labarai: Gwamnati Za Ta Ba Tashoshin Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo Lasisi

278
0
Shugaba Muhammadu-Buhari-2
Shugaba Muhammadu-Buhari-2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabbin tsare-tsare kan abubuwan da suka shafi sadarwa ciki harda bada lasisi ga tashoshin talabijin da radio na yanar gizo.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar masu yada labarai a Abuja.

A lokacin da yake amsa tambayoyin tawagar, ministan ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin dukkanin mai yiwuwa domin ganin ta sake fasalin bangaren yada labarai.

Ministan wanda ya yi alkawarin sanya kungiyar a cikin       aikace aikace da tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba, ya kuma yi alkawarin ba bangaren yada labarai cikakken iko.