Home Labaru Sauke Nauyi: Ministan Sadarwa Yace Akwai Jan Aiki A Gaban Sa

Sauke Nauyi: Ministan Sadarwa Yace Akwai Jan Aiki A Gaban Sa

991
0

Ministan sadarwa Aliyu Isa Pantami ya bukaci ma’aikatan sa su daura damarar samar da ayyukan da za su kawo ci gaba a Najeriya.

Ministan ya yi wannan kiran ne a ranar farko da ya shiga ofis a matsayin ministan sadarwa inda ya ce akwai babban aiki a gaban su, wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. 

Ya ce ma’aikatar sadarwa za tayi amfani da hanyoyin sadarwar zamani na ICT domin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 50 daga talauci.

Ministan ya yi kira ga ma’aikatansa da cewa su zage dantse domin samu damar cika aiki da Shugaba Muhammadu Buhari ya daura a kansu.

Pantami ya ce matsalolin da Najeriya ke fama dasu ba a boye suke ba, kuma bangaren sadarwa ICT, za ta taka muhimmiyar rawar wajen rage zaman kashe wando da sauran su.