Home Labaru Ilimi Matsalolin Tsaro: An Ja Hankalin Matasa Su Dawo Cikin Hayyacin Su

Matsalolin Tsaro: An Ja Hankalin Matasa Su Dawo Cikin Hayyacin Su

224
0

An yi kira ga matasa su maida hankali kan harkokin karatu domin su zamo masu amfani a cikin al’umma.

Sarkin Shagari Lowcost Alhaji Muhammadu Inuwa, ya yi kiran a lokacin da kungiyar kawo cigaban al’ummar Barnawa ta kai masa ziyarar bangirma a fadar sa.

Alhaji Muhammadu Inuwa, ya ce matasa su ne kashin bayan cigaban kowace irin al’umma dan haka ya zama wajibi a matsayin sun a manyan gobe su dawo cikin hayyacin su.

Ya ce matsalolin tsaro da ake fuskan ta a unguwanin da sauran yankuna matukar matasa za su ba kokarin gwamnati goyon baya to babu shakka cikin sauki za a shawo kan lamarin.

A jawaban su daban-daban shugaban kungiyar Abdullahi Sabitu, wanda sakataren ta Auwal Sani Na Allah, ya wakilce shi, da kuma kansilar Barnawa Bello Musa Mato, wanda daya ne daga cikin ‘ya’yan kungiyar sun mika godiya kan rin shawarwarin da sarkin yaba su.

Sun ce daman ziyarar ta neman albarka ce kan ayyukan da kungiya ta sa a gaba dan haka kugiyar ta kai irin wannan ziyarar ga sauran masu rike da mukaman sarauta kuma ta samu cikakken goyon baya da hadin kai.