Home Labaru Yabon-Gwani: Fani Kayode Ya Jinjina Wa Pantami Wajen Yaki Da ‘Yan Ta’Adda

Yabon-Gwani: Fani Kayode Ya Jinjina Wa Pantami Wajen Yaki Da ‘Yan Ta’Adda

18
0
Femi Fani Kayode, Tsohon Ministan Sufurun Jiragen Sama A Nijeriya, Kuma Jigo A Jam’iyyar, PDP
Femi Fani Kayode, Tsohon Ministan Sufurun Jiragen Sama A Nijeriya, Kuma Jigo A Jam’iyyar, PDP

Tsohon ministan sufuri Femi Fani Kayode, ya ce babu wani minista a Nijeriya da ya taba yi wa ‘yan ta’adda illa kamar ministan sadarwa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Fani Kayode, ya yaba wa Pantami a kan matakan da ya ke dauka tare da shugaba Muhammadu Buhari, dangane da munanan hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’addan da su ka addabi jama’ar jihar Zamfara.

Ya ce a ‘yan makwannin da su ka gabata, an samu gagarumin ci-gaba wajen hare-haren da sojojin Nijeriya ke kai wa ‘yan bindiga a Yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Fani Kayode, ya kuma yaba da matakan da gwamnonin jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto da Jigawa da Kebbi da Neja ke dauka, lamarin da ya fara karfafa wa al’ummomin yankin gwiwa.