Home Labaru Sabon Sarki: Mutane 43 Su Ka Mika Takardun Neman Sarautar Kontagora

Sabon Sarki: Mutane 43 Su Ka Mika Takardun Neman Sarautar Kontagora

28
0
Kontagora

Kwamishinan kula da Ma’aikatar kananan Hukumomi da Masarautun gargajiya ta jihar Neja Barista Abdulmalik Sarkin Daji, ya ce mutane 43 ne Su ka Mika Takardun Neman Sarautar Kontagora.

Barista Abdulmalik, ya ce masu zaben sabon Sarkin sun zabi Galadiman Kontagora don ya shugabanci shirin zaben sabon sarkin, yayin da aka kara wa’adin rufe karbar takardun neman sarautar zuwa ranar Jumma, domin a ba masu sha’awa da ke nesa damar shigar da takardun su.

Shugaban masu zaben sabon sarkin Alhaji Shehu Yusuf Galadima, ya ce za su gudanar da aikin su tare da jin tsoron tsoma bakin wwamnati ba, ya na mai cewa, gwamnati ta kan shiga batun zaben sabon Sarki ne idan ta ga an tauye hakin wani ko kuma an nuna rashin adalci.

Ya ce su na da hakkin zaben Sarkin da zai zama karbabbe, wanda al’ummar masarautar su ke so domin ci-gaban masarautar da ma jihar baki daya.