Home Labaru Kwalara: Mutane 100 Sun Mutu A Jihar Neja – Kwamishina

Kwalara: Mutane 100 Sun Mutu A Jihar Neja – Kwamishina

9
0

Kwamishinan lafiya na jihar Neja Muhammad Makusidi, ya ce cutar Amai da Gudawa ta yi sanadiyyar mutuwar matane 100 daga watan Afrilu zuwa yau a jihar.

Makusidi ya bayyana haka ne, yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron inganta amfani da dabarun bada tazarar haihuwa da ya gudana a garin Minna.

Ya ce rashin tsaftace muhalli da yin bahaya a fili na daga cikin dalilan da su ka sa cutar ta yi mummunar barkewa tare da yin ajalin al’ummar jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnati ta fara aikin wayar da kan mutane a kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar domin samun kariya, sannan ta zuba magungunan cutar a asibitocin jihar.