Home Labaru Kiwon Lafiya Yabon Gwani: Buhari Ya Jajen Mutuwar Mace Ta Farko Da Ta Fara...

Yabon Gwani: Buhari Ya Jajen Mutuwar Mace Ta Farko Da Ta Fara Tuka Jirgin Yaki

253
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jajenta wa ‘yan’uwan mace ta farko da ta fara tuka jirgin yaki mai saukar Ungulu a Nijeriya, wadda ta rasa ran ta sanadiyyar wani hadarin mota.

Tolulope Arotile ta rasu ne a jihar Kaduna ranar Talatar da ta gabata, bayan ta samu wasu munanan raunuka a kan ta.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya fitar, Buhari ya jaddada kwazon Arotile wajen yaki a fagen daga domin kare Nijeriya daga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, ya na mai cewa ba za a taba mantawa da kokarin ta ba.

Mutuwar Arotile ta girgiza ‘yan Nijeriya da dama, ciki har da babban hafsan sojin saman Nijeriya Air Marshal Sadiq Abubakar, wanda ya wallafa irin kokarin marigayiyar a shafin sa na Twitter.

Ya ce ta na da fasaha sosai, kuma ta taka muhimmiyar rawa a kokarin dakile ‘yan ta’adda a jihar Neja.