Home Labaru Kasafi: Gwamnati Ta Amince Da Kudirin Tsare-Tsaren Kashe Kudi Na Shekara Ta...

Kasafi: Gwamnati Ta Amince Da Kudirin Tsare-Tsaren Kashe Kudi Na Shekara Ta 2021-2023

140
0

Gwamnatin tarayya ta yi hasashen tsara kundin kasafin Naira tiriliyan 12 da biliyan 66 a matsayin abin da za a yi cikin shekaru uku masu zuwa.

Karamin ministan kasafi Clement Agba ya bayyana wa manema labarai haka, jim kadan bayan  kammala taron majalisar zartarwa ta kasa a Abuja.

Clement Agba, ya ce gwamnati ta yi lissafin kudin gangar man fetur a kan Dala 40, tare da hangen cewa a kowace rana za a hako ganguna miliyan 1 da dubu 600 a Nijeriya.

A cewar ministan, man da Nijeriya za ta saida a shekara mai zuwa ba zai kai na wannan shekarar ba, saboda sabon tsarin da kungiyar OPEC ta shigo da shi kwanan nan.

Ya ce Gwamnati za ta samo ragowar kudin da za a kashe a kasafin shekara mai zuwa ne ta hanyar cin bashi da makamantan hakan.