Home Labaru Martani: Matawalle Bai Bada Kudi A Gina Makaranta A Jigawa Ba –...

Martani: Matawalle Bai Bada Kudi A Gina Makaranta A Jigawa Ba – Bappa

163
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bada gudunmawar naira miliyan 100 domin gina jami’a a jihar Jigawa.

Zailani Bappa, Mai Magana da yawun gwamnan Zamfara

Mai Magana da yawun gwamnan Zailani Bappa ya karyata rahoton, inda ya ce gudunmawar da Matawalle ya bada gudunmawa ce ga kungiyar Izala da ke gina babbar makaranta a jihar.

Idan dai ba a manta ba, an wallafa labarin yadda Matawalle ya ba shugaban kungiyar Izala Sheikh Bala Lau gudunmawar naira miliyan 100, domin ci-gaba da ginin wata makaranta da kungiyar ke ginawa a garin Shinkafi.

Zailani Bappa, ya ce babu abin da ya hada gudunmawar Matawalle da jihar Jigawa, kungiyar Izala aka ba domin kammala makarantar da su ke ginawa a Shinkafi, wadda ake sa ran ta zama jami’ar musulunci nan gaba.