Home Labaru Sojoji Sun Kashe ‘Yan Binidiga Uku A Enugu

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Binidiga Uku A Enugu

11
0
Nigeria-Army

Dakarun sojin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yan bindiga uku a Jihar Enugu.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce sun kashe ‘yan bindigar da su ka kai wa ‘yan sanda hari a ranar Alhamis da ta gabata, a wani shingen binciken jami’an tsaro da ke kan babbar hanyar Okija zuwa Onitsha.

Ya ce ɓangaren dakarun rundunar Golden Dawn da aka tura Enugu, sun murƙushe ‘yan bindigar ne a wata musayar wuta da aka, wadda ta tursasa masu tserewa.

Kakakin ya kara da cewa, ‘yan bindiga uku aka kashe, waɗanda ke cikin mota biyu ƙirar Hilux da Hummer, yayin da wasu su ka tsere da harbin bindiga a jikin su.