Home Labaru ‘Ya Kamata Buhari Ya Sauke Hafsoshin Tsaro’

‘Ya Kamata Buhari Ya Sauke Hafsoshin Tsaro’

738
0
'Ya Kamata Buhari Ya Sauke Hafsoshin Tsaro'
'Ya Kamata Buhari Ya Sauke Hafsoshin Tsaro'

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta kasa NAAC ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta fatattakar shugabannin hukumonin tsaro domin ceto Nijeriya da gwamnatin sa daga abun kunya.

NAAC ta ba shugaba Buhari wannan shawara ce domin ya kubutar da gwamnatin sa daga kuncin zubar da jinin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da yi a fadin Nijeriya.

Shugaban kungiyar Yusuf Kazeem ya bayyana cikin wani  jawabi da ya gabatarda ya gudana a birnin Abuja, tare da cewa cigaba da barin jan akalar tsaro a hannun subabbar matsala ce, domin ba wata dabara da ta rage masu, lamarin da ya haifar da koma baya ga sha’anin tsaron Nijeriya.

A karshe Kungiyar ta yi zargin cewa, wata kullaliya ce masu rike da madafan iko a fadar shugaban kasa ta hana a tsige shugabannin tsaron, saboda wasu dalilai na son rai, amimakon su maida hankali wajen samar da ingataccen tsaro a Nijeriya.