Home Labaru Kiwon Lafiya COVID-19 Ta Kashe Dan Kwamitin Yakar Ta

COVID-19 Ta Kashe Dan Kwamitin Yakar Ta

503
0
Daya Daga Cikin ‘Yan Kwamitin Yaki Da Coronavirus Ya Mutu A Jihar Ekiti
Daya Daga Cikin ‘Yan Kwamitin Yaki Da Coronavirus Ya Mutu A Jihar Ekiti

Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya sanar da mutuwar daya daga cikin ‘yan kwamitin yaki da cutar Coronavirus da ke jihar mai suna Remi Omotoso.

Sakataren yada labaran jihar Yinka Oyebode ya bayyana haka a cikin wata  sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa Omotoso ya rasu a ranar Juma’a sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya nda yay i fama da ita.

Omotoso ya mutu ya na da shekaru 75 a duniya, kuma dan asalin  yankin Ayedun-Ekiti ne, kuma kwararren masani a kan harkokin  kudi, sannan mutun ne nagari, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta kara da cewa, duk da dumbin ayyukan da su ke sha wa marigayin kai, yakan bada lokacin sa da kudinsa da karfin sa wajen gyara rayuwar al’umar jihar, kuma a koda yaushe yakan  bada goyon baya domin samun mulki nagaria fadin jihar.